YANZU-YANZU: An farmaki ayarin Motocin Atiku Abubakar a hanyar Maiduguri

Advertisements

Rahotannin da ke shigo mana yanzu sun nuna cewa an farmaki ayarin motocin Atiku Abubakar a hanyar Borno, ya yin ziyarar yakin Neman zabensa a yau laraba.
Lamarin ya faru yau a laraba ne kamar yadda gidan Talabijin na AIT ta nuna cikin wani faifayin Bidiyo. Har yanzu babu tabbacin rasa rayuka ba, Amma rahoto yace an raunata wasu.
Tuni dai Magoya bayan Atiku Abubakar suka zargi Jam’iyyar mai ci ta Jihar Borno, da shirin dakilesu akan wannan taro da suke son gudanarwa a Jihar, sai dai har yanzu yayan Jam’iyyar basu ce komai ba.
A ya yin taron Atiku ya dauki Alkawura 5 a jihar Borno ciki har da ci gaba da tonon man fetur na jihar Borno, da inganta masana’antar Noma na jihar, tare da samar da tsaro, da kawo ci gaba tsakanin yankunan Adamawa, Taraba, Gombe, Bauchi, da jihar Yobe, da sauransu.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like