DA ƊUMI-ƊUMINSA: Ɗan Sanda A Jahar Katsina Ya Lashe Gasar Karatun Alkur’ani

Advertisements

Wani ɗan sanda ɗan jihar Katsina, ya zo na ɗaya a musabakar karatun Alkur’ani mai tsarki da rundunar ‘yan sanda ta shirya.
Ofisan ɗan sandan, Nawas Usman wanda ya fito daga garin Daudawa yankin karamar hukumar Faskari jihar Katsina, ya lashe gasar karatun Alkur’ani mai girma wanda rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta shiyar wa jami’anta inda ya zamo zakara a cikin sauran jami’an ‘yan sandan da suka shiga gasar.
Nawas ya sami kyaututtuka tare da lambobin yabo wanda Malam Ibrahim Daurawa ya jagoranci mika masa kyaututtukan.
Kusan duk shekara, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina na shiyar irin wannan musabaƙar ga jami’an nata don zaburar da su game da sanin littafin Allah Alkur’ani mai tsarki ga jami’anta Musulmai da ke aiki a fadin jihar ta Katsina.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like