WATA SABUWA: Tun da na hau mulki ɓan taba sayen wata ƙaddara ba – Inji Buhari

Advertisements

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce bai taɓa sayen wata kadara ba tun da ya zama shugaban Najeriya a 2015.
Buhari, wanda ya je Landan domin duba lafiyarsa, ya bayyana hakan ne bayan wata gana wa da ya yi da Sarki Charles III a ranar Laraba.
Ya ce duk kadarorinsa da ya mallaka ya same su ne kafin ya zama shugaban kasa, inda ya kara da cewa “ba shi da sha’awar mallakar kadarori barkatai”.
Buhari dai ya gana da Sarkin na Burtaniya a karon farko tun bayan hawansa karagar mulki a watan Satumba.
A jiya Alhamis, wani mai taimaka wa shugaban kasa, Tolu Ogunlesi, ya saka wani faifan bidiyo a shafinsa Twitter na shugaban kasar yana magana kan sakamakon tattaunawarsa da sarkin.
“Ya tambaye ni ko ina da gida a nan? Na ce ‘a’a’. Ko a Nijeriya, gidajen da nake da su, su ne wadanda nake da su kafin in shiga gwamnati.
“Ba ni da sha’awar mallakar dukiya barkatai. Na fi samun ƴanci idan ba ni da komai
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like