Advertisements
An gano wata babbar mota da ta lalace dankare da kudade yan naira dubu-dubu a soshiyal midiya A cewar bidiyon, babbar motar ita ce ta uku da aka dankarawa kudade daga wata jihar arewa ana neman inda za a juye su. Lamarin na zuwa ne yayin da babban bankin kasa wato CBN ya fara shirin sauya wasu kudade daga cikin takardun naira.
Wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya nuna wata lalatacciyar babbar mota cike da kudi yan N1,000 daga wata jihar Arewa. Kamar yadda mutanen da ke cikin bidiyon suka bayyana, wannan motar ta kai kimanin watanni biyu a wajen suna neman inda za a juye su.
Bidiyon ya nuno takardun nairori musamman yan N1,000 marasa kyau, wanda masu daukar bidiyon suka yi ikirarin cewa an ajiye su ne a wani wuri da ya rubar da su. Yanzu mamalakansu ke neman wurin da za su canja su da Dala.