Advertisements
Ministan harkokin cikin gida na Najeriya Mista Ra’uf Aregbosola, ya bada tabbacin kammala aikin ginin sabon gidan gyaran Hali na Janguza dake yankin karamar hukumar Tofa, Kafin nan da karshen shekarar da muke ciki ta 2022.
Mista Aregbosola ya bada wannan tabbaci ne, lokacin ganawarsa da manaima labarai a ziyarar da ya kawo nan kano domin duba yadda aikin ginin sabon gidan gyaran halin na Janguza yake gudana.
Advertisements