WATA SABUWA: Tinubu ne zai zama Shugaban Kasar Nijeriya a 2023 – Buhari

Advertisements

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023. Kamar yadda Daily  Post Ta Ruwaito.
Buhari yace APC tayi sa’ar samun Tinubu a matsayin dan takararta na shugaban kasa.
Ya yi magana ne a kasar Burtaniya yayin da yake mayar da martani kan yiwuwar APC ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Da aka tambaye shi kan yiwuwar APC ka iya yin rashin yin nasara a 2023?, Buhari ya ce: “Mene ne zai hana jam’iyyata ba za ta ci zabe ba? Za mu ci zabe.
“Tinubu, dan takarar shugaban kasa, sanannen dan siyasa a kasar nan, ya kasance gwamna na wa’adi biyu a jihar Legas, jihar da ta fi kowa arziki kuma jihar da aka fi ziyarta.
“Don haka, ina ganin jam’iyyar APC ta yi sa’ar samun shi ya zama dan takara.”
A watan Yuni, Tinubu ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC bayan ya doke mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
Tsohon gwamnan jihar Legas ya samu kuri’u 1,271 inda ya doke abokin hamayyarsa Amaechi wanda ya samu kuri’u 316.
Bayan bayyanar sa a matsayin dan takaran, wasu badakaloli da dama sun biyo bayan sahihancin sa na kasancewa ko zai iya mulkin Najeriya.
Duk da wadannan zarge-zargen, kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ta wanke Tinubu daga duk wani zarge-zarge.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like