ASIRI YA TONU: Killi bidiyon yadda aka kama wani ɗan Nijeriya da miyagun kuɗi a London

Advertisements

Hukumomi a kasar Burtaniya sun dura gidan wani dalibi dan Najeriya, inda suka gano tsabar kudi da suka kai $8.5m.
Kudaden da aka gani cikin nau’ikan daloli daban-daban an ajiye su ne a cikin wani akwati, kamar yadda yake a wani bidiyo.
Mutumin da aka kaman yana magana da daya daga cikin harsunan Najeriya, ya kuma bayyana cewa shi dalibi ne a kasar 
Burtaniya – Wani bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna lokacin da hukumomin kasar Burtaniya suka shiga gidan wani dalibi dan Najeriya, suka bankado wasu kudade masu yawa. 
Bincike yace an kama dalibin ne da wasu daloli a cikin akwati, yawansu ya kai akalla $8.5m. Bidiyon, wanda wani yanki ne na ayyukan kakkabe ta’addanci a Burtaniya, ya nuna dalla-dalla yadda aka dura gidan dalibin dan Najeriya da kuma yadda aka gano kudaden da ya boye 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like