Advertisements
Jama’ar yankunan da ‘yan bindiga suka addaba sun fito sun bayyana ra’ayinsu ga yunkurin sojoji na ayyana neman su Turji ruwa a jallo.
Sojoji sun sanya tukwici mai gwabi ga duk wanda ya ba da masaniyar da ta kai ga kame ‘yan ta’adda 19 a Najeriya Jihohin Arewacin Najeriya ne suka fi shiga tashin hankalin rikicin ‘yan bindiga a Najeriya a shekarun nan.
Wasu mazauna a jihar Zamfara a ranar Litinin sun bayyana shakku kan samun wani ci gaba a yunkurin sojoji na ayyana neman ‘yan ta’adda ruwa a jallo, Daily Trust ta ruwaito.
Sun kuma bayyana mamakin cewa, meye ya dauki sojojin Najeriya dogon lokaci kafin ayyana neman shugabannin ‘yan ta’addan ruwa a jallo ko kuma ma kokarin kama su da ransu.
Idan baku manta ba, wani rahotonmu na baya ya bayyana yadda aka ambaci wasu tsagerun ‘yan ta’adda 19 da sojoji suka ce suna nema ruwa a jallo tare da sanya tukwici mai gwabi ga wanda ya fallasa maboyarsu.