Advertisements
Rahoton Cadre Harmonise (CH) ya gargaɗi babban birnin tarayya Abuja, jihar Legas da ƙarin wasu jihohi 25 a Najeriya cewa da yuwuwar su fusakanci matsanancin rashin abinci da kayan gina jiki a shekara mai zuwa.
The Nation tace jihohin da rahoton ya yi hasashe sun haɗa da, Abiya, Adamawa, Bauchi, Benuwai, Borno, Kuros Riba, Edo, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, da Katsina. Sauran sune, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Filato, Ribas, Sakkwato, Taraba, Yobe, da kuma jihar Zamfara.
A cewar rahoton ‘yan Najeriya miliyan 25.3 ake hasashen zasu shiga matsalar rashin abinci a jihohi 26 tsakanin watan Yuni da Agusta, 2023.
Abuja, Katsina, Kano Da Wasu Jihohi 24 Wadanda Zasu Shiga Matsalar Abinci a 2023.
Daga cikin jihohin dake sahun gaba da yawam waɗanda matsalar zata shafa akwai Borno mai mutane miliyan 1.4m, Yobe da miliyan 1.3m da kuma Adamawa mai miliyan ɗaya cif.
Rahoton ya kuma bayyana cewa kusan ‘yan Najeriya miliyan N17m ne ke fama da rashin abinci yanzu haka ciki harda ‘yan gudun Hijira da kuma waɗanda aka maida gidajensu. Haka nan rahoton yace mutane 41,000 waɗanda a halin yanzun suke fama da yunwa zasu shiga matsanancin yanayin rashin abinci daga cikin yan gudun Hijira 83,000 a jihohin Benuwai, Taraba da Kuros Riba.