Advertisements
Kotun tarayya da ke Abuja ya zartar da hukunci a shari’ar Emmanuel Bwacha da Yusuf A. Yusuf Alkali ya ruguza zaben da aka yi wanda ya ba Sanata Bwacha takarar Gwamnan Taraba a APC Sanata Yusuf A. Yusuf ya ji dadin hukuncin da aka yanke cewa a sake shirya zaben ‘dan takara.
Babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja, ya soke zaben tsaida gwanin da ya ba Emmanuel Bwacha takarar gwamnan jihar Taraba.
Daily Trust tace Sanatan Taraba ta tsakiya, Sanata Yusuf A. Yusuf ne ya shigar da wannan kara a kan ‘dan takaransu, jam’iyyar APC da kuma INEC.
A ranar Litinin, 14 ga watan Nuwamba 2022, babban kotun tarayya ya yi fatali da zaben da jam’iyyar APC ta shirya na ‘dan takaran Gwamnan Taraba.
A watan da ya wuce wani babban kotun tarayya da ke garin Jalingo ya yanke irin wannan hukunci a sakamakon karar da David Sabo Kente ya shigar.
APC za ta sake shirya zaben gwani A duka shari’ar da aka yi, Alkalai sun umarci jam’iyyar APC ta sake shirya sabon zaben tsaida ‘dan takarar Gwamna da zai rike mata tuta a takaran 2023.