Da alamamun wasu daga cikin Gomnoni ba za su yi tafiyar Ɗan Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ba sabo da saɓanin da suka samu tsakaninsu

Advertisements

Jam’iyyar PDP ta gamu da rigingimun cikin gida iri-iri tun da Atiku Abubakar ya samu tiktin takara Akwai wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP musamman Gwamnonin jihohi da ke yakar ‘dan takaran na 2023.
 Gwamnonin sun gindaya sharudan da sai an cika sannan za su bada gudumuwa a zaben shugaban kasa.
Jam’iyyar hammaya ta PDP tana fama da rikici daga cikin gidanta yayin da ake shiryawa babban zabe a farkon shekarar badi. 
Akwai gwamnonin jam’iyyar da ke rigima da Dr. Iyorchia Ayu, kuma sun ce ba za su goyi bayan Atiku Abubakar sai an cika masu sharuda. 
Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom yana cikin manyan masu yakar Atiku Abubakar, har ta kai ya kira masu goyon bayan ‘dan takaran da makiyin jiharsa.
Tun kwanaki Mai girma Samuel Ortom yace ba zai taba goyon bayan Atiku a 2023 har sai ‘dan takaran ya nemi afuwarsa kan abin da ya faru tsakaninsu. 
Nyesom Wike bai ji dadin yadda zaben tsaida gwanin ta kaya a jam’iyyar PDP ba. Gwamnan na Ribas ya zo bayan Atiku Abubakar wajen samun tikiti.
 Gwamnan ya yi alkawarin ba zai taya Atiku yakin neman zaben shugaban kasa ba saboda zargin cewa ‘dan takaran bai dauki mutanen Ribas da daraja ba. 
Shi ma Seyi Makinde yana cikin gwamnonin da ke tare da tafiyar Nyesom Wike, yace dole sai an yi gyara a jam’iyyar PDP muddin ana so su taimaki Atiku. Kwanakin baya aka ji mataimakinsa ya halarci taron Afenifere, har ya shaidawa Duniya cewa Gwamna Makinde yana goyon bayan Bola Tinubu a 2023. 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like