Advertisements
Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki ta kasa tace akwai shirin janye tallafin man fetur Zainab Ahmed tace daga Mayun 2023,
.Gwamnatin tarayya ba tayi tanadin cigaba da biyan tallafi ba Ministar tayi wannan bayani a taron NESG, tace biyan kudin yana ci wa gwamnati tuwo a kwarya.
Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed, tace gwamnatin tarayya za ta daina biyan tallafin man fetur a shekarar 2023.
Vanguard ta rahoto Zainab Ahmed tana cewa daga Yunin 2023, gwamnatin tarayya ba za ta cigaba da kashe kudi saboda a saukake farashin man fetur ba. Ministar tarayyar ta koro wannan bayani ne a wajen taron NESC ranar Talata a garin Abuja.
Gwamnati ta dai kafe a kan maganar yin watsi da wannan tsari. Ahmed tace janye tallafin yana cikin tsare-tsaren gwamnati a kasafin kudin shekara mai zuwa.
Fetur Zai Iya Haura N400, Gwamnoni Sun Bada Shawarar Gaggauta Janye Tallafi Inda gizo ke sakar Kamar yadda This Day ta fada, Ministar tace babbar kalubalen da gwamnati za ta fuskanta shi ne yadda za a bi wajen janye wannan tallafi gaba daya.
Dole mu zauna da jama’a. Mun fara yin zama da jihohi da sauran mutane kafin a amince da hakan a tsarin tattalin arzikin kasa. Dole ne mu bi shi a hankali, mu na sanar da mutanen Najeriya irin makudan kudin da ake batarwa wajen biyan tallafin fetur.
Sannan kuma akwai bukatarmu wayar da kansu a game da abubuwan da muka gaza yi saboda ana daukar nauyin tallafin.”