Gwamnatin tarayya ta ƙara N30 kan kowani kwanon Abincn ‘yan Firamare don inganta shi a makarantun gwamnati

Advertisements

Jummaʼa, Nuwamba 18, 2022 at 4:25 Yamma daga  Aisha Khalid Gwamnatin tarayya tayi gyara kan tsarin ciyar da dalibai inda aka mayar daga N70 na kowanne dalibi zuwa N100 na abincinsu.
 Kwamishinan jin kai da walwala na jihar Delta yace gwamnatin tarayyan tayi hakan ne domin sake inganta nagartar abincin da daliban ke ci Ya rarrabewa masu girki kayan aiki wanda yace su yi amfani da nagartattun halayensu don su zame musu jagora wurin aikin da aka saka su.
 An sake duba shirin ciyar da yaran makaranta a Najeriya inda aka duba shi tare da kara N30 kan N70 na kudin abincin ‘yan makaranta a jihar Delta.
 Gwamnatin Tarayya ta Gyara Rangyem din ‘Yan Makaranta, Ta Kara N30 kan Kowanne Kwanon Dalibi. 
Hoto daga punchng.com Asali: UGC Punch ta rahoto cewa, kwamishinan jin kai da tallafi, Dakta Darlington Ijeh, wanda ya bayyana hakan a Asaba, ya bayyana takaicinsa kan yadda masu dafa abincin ke kauro.
 Ijeh, wanda aka Gwamna Ifeanyi Okowa ya rantsar a watan Augustan 2022, ya sha alwashin lura da shirin gwamnatin tarayyan domin inganta rayuwar jama’ar jihar. 
Bayan shigata ofis a watanni uku da suka gabata, na gaji wasu lamurran koma baya daga NHGSFP da ya hada da rashin biya kan lokaci, da sauran matsalolin da suka shafi masu girkin wadanda ke taba dalibai da jiha.
 “A yau an sake duba N70 na abincin kowanne ‘dan makaranta inda aka mayar N100 kowanne da kuma sauran matsalolin da suka addabi tsarin ciyar da ‘yan makaranta a jihar kamar rashin masu girkin da biya ba bisa tsari ba, sun zama tarihi.” 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like