TIRƘASHI: Shehu Sani ya yi wa gwamnatin Buhari izgili kan alkawarin da ta yi na tsamo mutum miliyan 100 daga talauci a kasar.

Advertisements

Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a jihar Kaduna ya yi wa gwamnatin Buhari izgili kan jefa yan Najeriya cikin talauci.
 .Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta hannun Ma’aikatar Kwadago da samar da ayyuka ta yi alkawarin tsamo yan Najeriya miliyan 100 daga talauci Sai dai a ranar Alhamis, hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar da alkalluma da suka ce yan Najeriya miliyan 133 sun fada matsananciyar talauci.
Legit.ng Hausa ta ruwaito
Sanata Shehu Sani ya yi wa gwamnati mai ci yanzu izgili saboda gazawarta na tsamo yan Najeriya miliyan dari daga talauci a maimakon hakan ta jefa mutane miliyan 133 cikin mummunan talauci. 
Tsohon sanatan na Kaduna ta tsakiya ya bayana hakan ne cikin wani rubutu da ya saki a sahihin shafinsa na Tuwita a ranar Juma’a 18 ga watan Nuwamban shekarar 2022.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like