Ma’aikata sashin Shari’a a Nijeriya sun bukaci da Shugaba Buhari ya amince a yi musu ƙarin albashi

Advertisements

.Ma’aikata sashin Shari’a a Nijeriya sun bukaci da Shugaba Buhari ya amince a yi musu ƙarin albashi
Ma’aikatan kotunan Najeriya suyi shewa, shugaba Buhari ya amince a yi musu karin albashi Ministan Shari’a yace an umurci ma’aikatar biyan albashi (RMAFC) ta gaggauta aiwatar da wannan tsari Bangaren Shari’a na daya daga cikin sassan gwamnati uku masu zaman kansu amma duk da haka suna kukan karancin albashi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da karin albashi ga ma’aikatan shari’a a Najeriya. Shugaban kasan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a birnin Fatakwal, jihar Rivers, yayin bikin kaddamar da sabon makarantar lauyoyi da gwamna Nyesom Wike ya gina. 
Buhari ya samu wakilcin Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN, rahoton ChannelsTV. Malami ya bayyana cewa Shugaban kasan ya amince da karin albashin ne saboda baiwa ma’aikatan Shari’a karfin zaman kansu da kuma wanzar da gaskiya.
Shugaban kasa ya amince da karin albashi da ma’aikatan shari’a kuma tuni an umurci shugaban hukumar biyan albashi da ofishin Antoni Janar na tarayya da ministan shari’a su fara tsarin aiwatar da karin.” 
Laget.ng Hausa ta ruwaito.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like