Shin kun san Illar da ke cikin Amfani da Afilikeshin na GBWhatsApp musamman ga masu ta’ammuli da Yanar Gizo

Advertisements

Da yawan mutane su na amfani da wannan APK ɗin mai suna a sama, ba tare da sun san illar da ke tattare da amfani da shi ba.
Su dai kawai sun san cewa suna da ikon da za su yi abubuwa da yawa wanda sauran Manhajoji ba su yi!
Na farko yana da kyau mutum ya san cewa, ita wannan Manhaja ta GBWHATSAPP babu ita a Play Store, kuma duk APK ɗin da babu a Play Store to ka sani cewar ba shi da License kenan, bai zama Trusted App ba, sannan za’a iya samun cutuwa ta hanyar amfani da shi.
GBWhatsapp manhaja ce da wasu ƴan damfara su ka ƙirƙiro domin su yaudari Al’umma ta hanyar kwasar dukkan wasu sirruka da ke cikin wayarsu, idan ba haka ba, me ya sa babu shi a Play Store? Wannan dalilin ne ya sa a ka saka masa features da yawa ma su burgewa yadda idan ka fara amfani da shi ba zaka iya dainawa ba!
Na san wani zai ce “to gashi ni ina amfani da shi amma kuma babu abinda ya faru da ni” to ka sani Masu amfani da shi suna da yawa sosai a yanzu, shi ya sa ka ga har yanzu abun bai zo kanka ba, amma duk na farko-farkon da su ka fara amfani da shi lallai yanzu duk sun zama Victims.
Kaɗan da ga cikin abinda za’a iya kwasa a cikin wayarka madamar GB ya na Installed a cikin wayarka sune:
Contact ɗinka
Chat History naka
Da kuma dukkan wasu Codes da kake Generating da ga wasu platforms, saboda haka hatta da Acc Details naka madamar suna cikin wayarka to ba su da shamaki da su! Kai a taƙaice dukkan abinda ke cikin wayarka zai zamana za su iya controlling ɗin shi madamar wannan manhaja ta na Installed a wayarka.
Wannan ne ya sa ko a wajen ɗaukoshi (Download) ma za ka ga sun gaya maka cewar “this type of file can harm your device do you want keep GBWhatsApp Anyway? Kai kuma sai ka danna yes wato ka yarda duk abinda zai faru ya faru! Kuma alhali sun sanar da kai cewa akwai cutuwa a ciki!
Sannan idan mu ka duba ta fuskacin mu’amala za muga sam ya saɓawa tsari da yanayin mu’amalarmu, duk wanda ya ke amfani da shi ya san me ni ke nufi.
Saboda haka ina mai ƙara ankarar da ƴan’uwa akan cewa a gujewa amfani da wannan Manhaja mai haɗarin gaske, kafin ranar da za mu yi da na sani.
Ga wanda ya ke son ƙarin bayani yana iya ƙara faɗaɗa bincikenshi a kai.
– Abou Najmah
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like