Sojojin sun yi ruwan wuta ga yan ta’adda, sun kashe da dama a Zamfara da Kaduna

Advertisements

Rahotanni daga Najeriya na cewa sojoji sun kashe ‘yan bindiga da dama a hare-haren sama da suka kaddamar kan maɓoyarsu a jihohin Kaduna da Zamafara.

KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin tarayya za ta bayar da bashi ga masu kananun sana’o’i dubu 98 a Nijeriya

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta rawaito cewa a Kaduna, sojojin sun kai harin ne kan wani shugaban ‘yan bindiga Alhaji Gana a karamar hukumar Kinandan, da Ali Kawaje da Musa Pajelo da Kachalla Bello a Birnin Gwari.

An kuma tarwatsa ‘yan bindiga kuma a yankin Walawa da Fadaman Kanauta da Kuduru, kamar yada jaridar ta ambato Samuel Aruwan na cewa.

Advertisements

A WANI LABARIN KUMA: YANZU-YANZU: An garzaya da Aisha Buhari Asibiti, sakamakon karaya da ta samu a kafa

A Zamfara kuma jiragen sojin Najeriya sun yi luguden wuta a yankin Shinkafi. Kakakin sojojin Najeriya Edward Gabkwet ya ce jami’ansu na cigaba da daukar matakai fatatakar ‘yan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya.

Hare-haren saman na zuwa ne kwanaki bayan ‘yan bindiga sun kashe mutum 44 a Zamfara.

Yankin arewacin Najeriya na fama da hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane domin kudin fansa a shekarun baya-bayanan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like