Mutumin da ke yin basaja a matsayin Mace ya samu wajen zama a gidan gyaran hali

Advertisements

Wani magidanci a jihar Adamawa, Muhammed Abubakar mai shigar kayan mata ya na neman kudi a hannun mutane ya shiga hannun hukuma.

Muhammed, wanda ya yi Diploma kan harkokin kasuwanci daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Adamawa, Yola, ya ce ya na yin ado kamar mace kuma ya na bin mata da sunan shi mace ne.

Muhammed wanda dan asalin garin Tashan Sani ne a karamar hukumar Yola ta Kudu kuma mai suna Fadi, ya bayyanawa wata babbar kotun majistare dake Girei kusa da babban birnin jihar Yola cewa, ya na aiki tare da abokansa mata.

Advertisements

Ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi ne bayan da dan sanda mai shigar da kara, Wamkai Ngapuro ya gurfanar da shi a gaban kotu.

An bayyana cewa bayan ya na samun kudi tsakanin Naira 500 zuwa Naira 1, 500, bisa la’akari da kudin da suke samu daga wurin maza a rana.

Babban Kotun Majistare, karkashin jagorancin Martina Gregory, bayan da ya amsa laifinsa, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan yari har zuwa ranar 5 ga Disamba, 2022

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like