Advertisements
Tsohon Sarkin Kano kuma jagoran Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya umarci mabiyansa su zabi Uba Sani ya zama gwamnan Kaduna.
A wurin taron shekara-shekara a Kaduna, Sheikh Tijani Inyass yace Khalifa ya umarci su mara wa APC baya a Kaduna, ya kuma gaya musu wanda zasu zaɓa a Kano.
DUBA WANNAN LABARIN: Za a samu yawaitar Bokom Haram a Nijeriya kamar hasken rana – Inji Obasanjo
Kaduna – Tsohon Sarkin Kano kuma jagoran Ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya, Khalipha Muhammad Sanusi II, ya nuna goyon bayansa ga ɗan takarar gwamnan Kaduna a inuwar jam’iyyar APC.
Sheikh Tijjani Sani Auwal Inyass, ɗaya daga cikin masu faɗa aji a Ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya ne ya bayyana haka a taron shekara na farko na ƙungiyar Tijanniya Grassroots Mobilisation and Empowerment (TIGMIEN)