Advertisements
Sakon banki na bogi, wata dabara ce da ‘yan damfara ke amfani da ita domin su cuci mutane su kwashe musu kudade, ko kuma ayi musu wata hidima a ‘yan shekarun baya, wanda yanzu ma aka dawo da ita.
Bincike ya nuna cewa, mutane da yawa sun fada tarkon wadannan masu damfara, ta hanyar sakon banki na bogi. Wadansu da yawa kuma suma suna afkawa cikin wannan zamba, saboda rashin sani.
A wannan rahoto, zamu bayyana hanyoyi guda uku wadanda za’a iya gane sakon banki na bogi, domin kada yan damfara su sami damar yi muku sama da fadi da kudaden ku.
Ga hanyoyin wadanda za’a iya gane sakon banki na bogi kamar haka
1. Zaka ga adadin kudin ka bai karu ba
Advertisements
Idan aka yi maka sakon banki na sanya kudi, nan take kudin ka na asusu, samammu, wato (available balance) suke karuwa. Amma a yanayin da kaga an yi maka sakon banki a wayar ka amma bai canza adadin kudin ka na samammu ba wato ( available balance ) to wannan sako zai iya zama na bogi. Shi sakon kudi na gaskiya yana shigowa wayar ka, to samammu ma, wato (available balance) zasu canza.
2. Sakon banki na bogi, baya zuwa da samammu (available balance )
Sassaukar hanya ta biyu ita ce, da zarar sako ya shigo, ka duba Idan na bogi ne to ba zaka ga main balance da available balance a cikin sakon ba, sai dai kaga ko gandarin kudin da aka turo maka ko kuma kaga available balance shi kadai. Wannan ma sakon na bogi ne. Sakon gaskiya yana zuwa ne da duka balance din, wato da gandarin kudin da aka turo maka da kuma available balance a kasan shi.
3. Rashin ganin sakon e-mail
Idan anyi hada-hadar kudi ta baki ta ajiyar kudi ko daukar kudi, to ana tura sakon zuwa adireshin ka na e-mail, musamman idan ka cike wa asusun naka adireshin email din, a yayin da ka bude asusun. Idan aka turo maka kudi na gaske, to za’a tura sakon zuwa email dinka, idan kuwa baka ganshi a email dinka ba to lallai ka da ka sakankance cewa kudi ya shiga asusun ka.
Wadannan sune hanyoyi uku da zaku gane sakon banki na bogi, sai ayi hattara.