Advertisements
CIWON HAQORI
A Sami Itacen Tumfafiya A Dafa Da Jar Kanwa a Kuskura da Dimin Shi Safe da Yamma Har Kwana 3,
Haqora Zaa Warke,
KOGON HAQORI
A dibi Audugar Cikin Kwallon Tumfafiya a Dangwali Nonon ta Kadan a Sa Cikin Kogon, A Riqa Yin Haka Lokaci-Lokaci, Kogon Zai Cike, (Amma fa Akwai Zafi)
TSUTSAR HAQORI
A Tafasa Saiwar Tumfay a Kuskura da Dimin Shi, Sau 3 A Rana Kwana 2,
Zaka Rabu da Ita,,
HAQORA MAI JINI
A Dafa Sassaqen Tumfafiya da Ganyen ta A Sa Gishiri Kadan, A Kuskura Baki da Dumi-Dumi Sau 3 A Rana Kwan 1 Zaayi,
Haqora Za Su Daina Jini
WARIN BAKI
A Dafa Furen Tumfafiya da Kwallon Ta Idan Ruwan Ya Huce A Sa A bin Wanke Baki (Brush) Ana Wanke Bakin Bayan an Dan Guntsi Ruwan
Kayi Ban Kwana da Doyin Baki,
HASKEN HAQORA
A Shanya Furen Tumfafiya Idan Ya Bushe A Maida Shi Gari A Hada Shi da Alaf Kadan, A Dan Gwala da Buroshi ko Asuwaki A Wanke Baki,
Haqora Za suyi Fari Tas,
DATTIN GORO KO HAYAQIN TABA
A Dafa Furen Tumfafiya da Lemun Tsami (Lime) A Wanke Baki Dashi da a bin Wanke Baki (Brush)
Dattin Zai Fita Daga Baki Gaba daya
Allah yasa mu dace Amen