Hukumar Zabe INEC ta gindaya dokoki da ƙa’ida domin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa, Gwamna da ‘yan Majalisu

Advertisements

Hukumar INEC mai shirya zabe ta saki jerin dokokin yakin neman zaben shugaban kasa, gwamna da yan majalisa Yan siyasa masu neman kujerun mulki daban-daban sun kaddamar da yakin neman zabe gadan-gadan. 
A ranar Alhamis jirgin yakin neman zaben APC ya garzaya Ebonyi yayinda na PDP ya shirga Ilori.
Yayinda ake saura watanni uku zaben 2023, hukumar gudanar da zaben kasa mai zaman kanta, INEC, ta fitar da jerin dokokin yakin neman zabe ga jam’iyyun siyasa da daukacin jama’a. 
A takardar mai shafi shida da INEC ta fitar, ta haramta zage-zagen juna da tsokanar fada a wajen kamfe kuma an hana tallata wani dan takara a wuraren Ibada, rahoton Channels. Hakazalika hukumar ta kara da cewa jami’an tsaro kadai aka hallatawa rike makami wajen taron kamfe.
 
A cewar INEC, wadanda aka amince su rike bindige sune yan sanda ko mambobin hukumomin tsaro da aka tura wajen kamfen musamman. 
Ga Ƙa’idojin Inji INEC
1 “Kada ayi kamfe a cibiyoyin Ibada, ofishohin yan sanda da ofishohin gwamnati.” 
2 “Kada a yi amfani da kalaman batanci kan juna wajen yakin neman zabe.” 
3 “Kada wani dan takara ko jam’iyyu su yi amfani da ofishohin gwamnati ko da na jarida ne” 
INEC tace manufar tarukan kamfe shine baiwa yan takara daman sanar da al’umma manufofinsu da abubuwan da suke shirya yiwa mutane. 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like