Advertisements
Wata mata yar kasar Indiya mai suna Mujhaycryaraha ta bayyana cewa ta shiga Addinin Musulunci bayan ta halarci kallon wasan ƙwallon ƙafan na cin kofin duniya da aka gabatar a Kasar Qatar.
Ga abinda ta bayyana “Na koma addinin Musulunci a birnin Doha, na kasar Qatar, Bayan nazo nan ne domin na kalli gasar cin kofin duniya amma bayan ganin yadda Musulmai suke gudanar da dabi’un su cikin girmamawa hakan yasa naji cewar a baya ban hau layi na gaskiya ba”