Advertisements
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, rashin godiyar Allah ce tasa har yanzu Atiku ya kasa hakura yake ta fitowa takarar shugaban kasa.
Advertisements
Yace Atiku yayi takara a ACN, yayi a PDP kuma tun shekarar 1999 yake takara amma ya kasa hakura.
Yace dan haka mutane su yi amfani da katin zabensu su masa ritaya.
Tinubu ya bayyana hakane a wajan yakin neman zabe a Legas.
Ya kuma bayar da tabbacin zai dora daga inda shugaba Buhari ya tsaya a ayyukan raya kasa.