Akwai Akasi cikin Maganar Taheer Fage, domin ina da Asibitin da ake kwantar da marasa lafiya – Inji Mawaki Rarara

Advertisements

Ni na manta ma lokacin da Taheer Fage yazo wurina, idan ma yazo to an taimaka masa, domin inda Asibiti tawa da ake yiwa marasa lafiya Magani – Inji Mawaki Rarara.
Fitaccen Mawakin Jam’iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara ya musanta maganar Jarumin Kannywood Taheer Fage, da yace ya bashi Naira dubu 20 a lokacin da bashi da Lafiya.
Rarara ya musanta maganar ya yin da DCL Hausa take zantawa dashi a ranar Asabar.
Idan ba a manta ba dai a watannin baya Jarumin Kannywood Taheer Fage ya bayyana cewa ya yin da bashi da Lafiya yaje neman taimako wajen Rarara, amma ya bashi Naira dubu 20, inda ake neman dubu 260 saboda za ayi masa aiki.
Sai dai Rarara yace daga shekara ɗaya zuwa yanzu duk wani ɗan Film da bashi da Lafiya to suna taimaka masa, yace har Asibiti yake da ita ta kansa, wanda ake taimakawa marasa Lafiya a wajen.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like