FASAHA: Yadda zaku yi Updating na wayar ku ta Android.

Advertisements

Shiga Setting ɗin wayar ka, bayan ya buɗe maka jeka cen ƙasa wurin da aka rubuta System shiga wurin, daga ƙasa zakaga wurin da aka rubuta System Update danna wurin, zakaga ya buɗe ya nuna maka Online Update da Local Update, sai ka danna Online Update, ka tabbatar ka buɗe data ɗin wayarka a ƙalla ka tabbatar kanada 20mb haka, kana shiga zakaga ta nuna maka wurin da zaka danna kayi Updating wayar naka.. 
Kana dannawa zata fara updating ka tabbatar kanada Enough caji a ƙalla sama da 50%.
Meyasa zakayi ma wayarka Updating?
Yi ma waya updating yana ƙara mata Speed wato sauri wurin gudanar da ayyuka, haka zalika wayarka ko matsalar rashin space take dashi indai zaka jure updating ɗinta zakaga space ɗin yana ƙaruwa, sannan duk wata matsala da wayar take baka yi mata Updating yana warware wasu matsalolin wayar ta dawo normal.. Yana rage shan cajin waya da sauran ƙananun abubuwa.
Kuma yin updating ɗin waya baya goge komai na waya, babu abinda zai goge a wayarka dan kawai kayi updating ɗinta.
Note: idan tafara updating ɗin tana ɗaukar tsawon lokaci a ƙalla 30 minutes wata kuma 15minutes ma tagama, bayan ta gama Downloding na Updated Version ɗin zatayi Restarting kanta, daganan zata kawo da kanta nan ma tana ɗaukar lokaci daganan tana gamawa zata maka Congratulation.
Allah yasa mu dace.
-Daga Bin Muhammad Alpotiskumy
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like