Duk Duniya babu wanda ya kai ƴan Nijeriya yawon kai ƙara Kotu – Alkalin Alkalai ya koka

Advertisements

Alkalin Alkalan na Ƙasa, CJN, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya yi ƙorafin cewa ƴan Nijeriya, musamman ƴan siyasa su ne suka fi kowa kai ƙara kotu, inda hakan ke wahalar da ɓangaren shari’a.

DUBA WANNAN: YANZU-YANZU: Kotu ta yanke wa IGP hukuncin daurin watanni 3 a gidan yari.

Mai shari’a Ariwoola ya bayyana hakan ne a yau Litinin a Abuja, a wajen taro na musamman na kotun koli da aka gudanar don bikin shiga shekarar shari’a ta 2022/2023 da kuma rantsar da sabbin manyan lauyoyi 62 na Nijeriya, SAN.

Advertisements

A WANI LABARIN KUMA: YANZU-YANZU: Tinubu ya fitar da Account Numbar da Talakawa za su tura masa kuɗi domin lashe zaɓen 2023.

A cewar CJN, a duk ‘yar rashin jituwa, sai mu garzaya kotu, kuma a duk shari’ar da ba mu samu nasara ba, sai mu garzaya kotun daukaka kara har zuwa Kotun Koli, komai kankantar taƙaddama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like