Ya kamata a gurfanar da Aisha Buhari Kotu, saboda ta ci zarafin Ɗalibi, Cewar Naja’atu

Advertisements

Najatu Mohammed, Kwamishiniya a Hukumar kula da Ayyukan Ƴan sanda, PSC, ta bukaci a gurfanar da uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari a gaban kuliya bisa laifin duka da kuma bayar da umarnin tsare wani dalibi, wanda ke shekarar karshe a jami’ar tarayya dake Dutse, Aminu Mohammed, da kuma tsohuwar hadimar ta kan kafafen sadarwa na zamani, Zainab Kazeem.

Jami’an ƴan sandan farin kaya ne su ka kama Mohammed tare da azabtar da su saboda sukar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari a shafinsa na Twitter, yayin da aka kama Kazeem ita kuma tare da lakada mata duka bisa zargin ta da fallasa sirrin.

A wata hira da jaridar DAILY NIGERIAN, Misis Mohammed ta caccaki uwargidan shugaban kasar kan abinda ta kira da ɗaukar doka a hannunta, inda ta yi kira ga jami’an tsaro da su kama ta tare da gurfanar da ita a gaban kuliya.

Ta ce dole ne dukkan ‘yan Najeriya su yi Allah-wadai da matakin Aisha Buhari.

Advertisements

“Ba ta da ‘yancin yin hakan. Hasali ma ya kamata a tuhume ta da aikata hakan. Ta dauki doka a hannunta. Ta dauki matsayi da nauyin babban kwamanda.

“Ina ganin ya kamata ‘yan Najeriya su tashi su ce a’a. Ba za mu ƙara yarda da wannan zalunci ba.

“Buhari ya bar wani giɓi a harkar mulki, shi ya sa kowane irin mutum ya samu damar shiga gwamnati.

“Ka ji fa, matar da ta ke ƙorafin cewa Mamman Daura ya karbe ragamar mulkin mijinta, amma yanzu ta zama azzaluma. A bayyane ta ke cewa ba don Allah da kuma ƴan kasa ta yi wannan maganar ba, sai dai son ran ta,” inji ta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like