Zan kayar da Tinubu da gaggawa, zan kawo ƙarshen Mulkin APC a Najeriya a 2023 – Atiku

Advertisements

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Abubakar Atiku, ya sha alwashin kayar da takwaransa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a zaben 2023.
Atiku ya yi wannan alkawarin ne a wajen taron jam’iyyar da aka gudanar a Akure, jihar Ondo a ranar Laraba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce yana da yakinin cewa jam’iyyar adawa za ta lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Atiku ya ce idan har aka zabe shi, gwamnatinsa za ta samar da isassun kudade na ilimi, yana mai addu’ar cewa ‘yan Najeriya ba za su taba ganin sake dawowar gwamnatin APC fiye da 2023 ba, lamarin da ya ce ya jawo wa ‘yan Nijeriya wahalhalun da ba a taba gani ba.
Ya koka da halin da ilimi ke ciki a kasar, ya kuma zargi jam’iyya mai mulki da tabarbarewar manufofinta na ilimi. Ya sha alwashin cewa ba za a rufe jami’o’in Najeriya ba saboda yajin aikin da malamai ke yi kamar yadda suke a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like