Kotu ta bada umarni sakaye COAS bayan ta garƙame Shugaban Hukumar EFCC da Sufetan ‘Yan Sanda

Advertisements

Kotu ta samu Janar Faruk Yahaya da laifin raina mata hankali, don haka an yanke masa hukuncin dauri Alkali Halima Abdulmalik tace a tsare Shugaban hafsun sojojin kasan a gidan gyaran hali a Minna A hukuncin da aka zartar a jihar Neja, an samu Manjo Janar Olugbenga Olabanji da laifin raina kotu.
 
Babban kotu da ke zama a garin Minna a jihar Neja, ta bada umarnin a kama shugaban hafsun sojoji na kasa, Janar Faruk Yahaya.
 A rahoton da aka samu daga gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba, an samu baban sojan kasan da laifin raina kotu. Baya ga Janar Faruk Yahaya, Alkalin da ta saurari shari’ar, Halima Abdulmalik ta bukaci a cafke shugaban TRADOC, Olugbenga Olabanji. 
An samu Manjo Janar Olugbenga Olabanji da irin laifin da shugaban sojojin kasar ya aikata. Daily Post ta tabbatar da wannan rahoton.Read more: https://www.gulfnett.com/2022/11/munyi-anfani-ta-wayar-da-aminu-adumu.html
Mai shari’a Halima Abdulmalik tayi amfani ne da wata dokar aikin gwamnatin jihar Neja ta shekarar 2018 wajen zartar da wannan hukunci.
 Kotu tace wadannan mutane biyu da ake tuhuma, sun sabawa umarnin da ta bada a ranar 12 ga watan Oktoba 2022, wanda yin hakan laifi ne. 
Halima Abdulmalik ta bukaci a tsare Janar Yahaya da Manjo Janar Olabanji a gidan gyaran hali da ke garin Minna har su iya wanke kansu. 
Kotu ba za ta zauna ba sai makon gobe Bayan ta zartar da wannan hukunci, Alkalin ta daga shari’a zuwa mako mai zuwa. Sai ranar 8 ga wata za a cigaba da sauraron karar a kotu. Har zuwa yanzu ba a ji wata sanarwa ta fito daga gidan soja a kan wannan hukunci da aka yi wa Janar Faruk Yahaya da Janar O. Olabanji ba. 
Daga: Legit Hausa
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like