Advertisements
Adamawa – Rahoton da muke samu yanzu haka ya nuna cewa wasu Motocin dake cikin Ayarin gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, sun yi hatsari.
Jaridar Punch ta tattaro cewa mutane hudu sun rasu a mummunan hatsarin wanda ya rutsa da motar Toyota Hilux ɗauke da ‘Yan Banga dake wa gwamnan rakiya.
Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya auku da Motar ne a Fadamareke, ƙaramar hukumar Hong, yayin da gwamnan ke kan hanyar zuwa garin Mubi domin halartar wani taron yakin neman zaɓe.