An samu raguwar yawaitar mutuwa daga 264,463 zuwa 51,000 kan masu cuta mai karya garkuwar jiki HIV – Boss Mustapha

Advertisements

Sakataren gwamanatin tarayyar Najeriya Boss Mustapha ya ce mutanen da ke mutuwa sanadiyyar cuta mai karya garkuwar jiki sun ragu a ƙasar.
A lokacin taron tunawa da ranar yaƙi da cutar AIDS ta duniya, wanda ya gudana ranar Alhamis a Abuja, Mustapha ya ce mace-mace sun ragu daga 264,463 a 2015 zuwa 51,000 a bana.
Haka nan ya bayyana cewa an kuma samu raguwa a yawan mutanen da ke kamuwa da cutar.
Sakataren na gwamnatin tarayya ya buƙaci majalisun dokokin jihohi su amince da dokar haramta tsangwamar masu cutar HIV domin ɗorewar nasarar da ake samu wurin yaƙi da cutar.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like