Advertisements
Rundunar Sojin Najeriya ta ce, Sojoji sun kashe ‘yan ta’addar Boko Haram a Borno, sun kwato manyan bindigogi da makamai
Advertisements
Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun Operation Hadin Kai sun kashe wasu ‘yan kungiyar ta’adda ta Boko Haram/Daular Islama a yammacin Afirka.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka fitar a shafin Twitter na rundunar sojojin Najeriya a ranar Juma’a.
A cewar rundunar, an kashe ‘yan ta’addan ne bayan wani samame da suka kai a kusa da hanyar Wajiroko zuwa Damboa a jihar Borno.
A WANI LABARIN KUMA: Za mu fara zanga-zanga ranar Litinin idan ba a saki Aminu Muhammad ba – In ji kungiyar daliban Najeriya ta NANS
Kayayyakin da aka kwato daga hannun ‘yan ta’addan sun hada da manyan motoci da makamai da alburusai.