Majalisar Kula da bunƙasa Tattalin Arziki a Nijeriya (NEC) ta miƙa Aniyarta wa (FEC) kan sauya tsarin Dokokin Kuɗi

Advertisements

Majalissar Kula Da Tattalin Arzikin Kasa (NEC), Ta Mika Kudirin Doka Gaban Hukumar Zartarwa Kasa (FEC) kan Sake Fasalin Dokokin Kudi Ministar Kudi Da Kasafi A Nigeria Ta Sanar Da Aike Sabon Daftarin Tsarin Dokokin Zuba Hanun Jari Na Shekarar 2023 A Tsakiyar Watan Da Ya Gabata Gwamnati Ta Kaddamar Da Sabbin Kudaden Da Yan Kasar Zasu Ringa Amfani Da Su.
 Zainab Ahmed wacce take ministar kudi da kasafi ta ce akwai tanadin haraji akan kudaden cryptocurrency da sauran hada-hadar kudi a cikin kudirin sake fasalin dokokin kudi na 2022.
 A wata sanarwa da Laolu Akande, mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya fitar, yace ministar ta bayyanwa majalisar tattalin arzikin kasa (NEC) abinda kudirin ya kunsa a taro majalissar na musamman da aka yi ranar Alhamis din nan. Jaridar The Cable ta rawaito cewa ministan ta ce kudurin dokar da za’a gabatarwa majalissa an dora ta ne kan wasu tsare-tsare guda biyar. Ta ce tsarin dokokin da ake son gabatarwa din akan haraji zasu samar da ayyukan yi, haɓakar tattalin arziki, da kuma sake fasalin yadda ake samun kudin shiga a Nigeria da yadda ake tassarufi da su.
 
Ta ce kudurin dokar ya nemi yin gyara kan kudaden shiga da kuma ka’idojin karbar haraji da kuma wasu sauye-sauyen akan habaka tattalin arziki. Zainab tace kudirin yana nufin yin gyara da kuma tanadin dokoki dangane da yadda ake tafiyar da harkokin kudi na gwamnatin tarayya.
 “Alal misali, a ƙarƙashin ginshiƙin kudin Harajin, za a shigar da dukkan sassan tattalin arzikin cikin, kamar wanda suka haɗa da Harajin Samar da Kuɗi daga cinikaiyar yana gizo da kuma hada-hadar kudi na cryptocurrency”.
Hakazalika, a karkashin dokar akwai kudirin doka kan bangaren hakar iskar gas da kuma rage kudin shiga daga fitar da iskar da ake yi” Karƙashin kudirin da kuma gyare-gyare dokokin harajin za a lamunin zuba hannun jari; canje-canje wajen habaka hakar mu’amalar kudin kasashen waje da kuma inganta yanayin kudin kasa.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like