ABUN A YABA: Masarautar Kazaure ta raba Naira Miliyan 10 ga mutane 3200 a yankin

Advertisements

Mai magana da yawun masarautar, Malam Gambo Garba ne ya bayyana haka a tattaunawarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Juma’a a Dutse, babban birnin jihar.

Malamin ya ce an rabar da kudin ne ga wadanda suka cancanta a gundumomi tara da ke masarautar.

DUBA WANNAN: YANZU-YANZU: Bayan an saki Aminu, zai gana da Shugaba Buhari a Villa cikin daren nan

Advertisements

A cewar Garba, Shugaban Kwamitin Tara Zakka na Masarautar, Alhaji Bala Muhammad, ya ce, nan ba da dadewa ba za a fadada raba zakkar da aka tara zuwa ga majinyatan da ke asibitoci daban-daban a yankin Kazaure.

A WANI LABARIN KUMA: Yan Kungiyar ISWAP 210 sun mika wuya bayan da Sojoji suka kashe ‘yan ta’adda 44

Garba ya kara da cewa, Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Hussaini, ya ba da tabbacin masarautar za ta ci gaba da ba da himma wajen karba da kuma raba Zakkar kamar yadda addini ya tanadar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like