Anya kuwa dagaske Gwamnatin Nijeriya ta shirya kashe Ni – Inji Ɗan ta’adda Bello Turji

Advertisements

Bello Turji Kachalla, wanda aka fi sani da Turji, fitaccen dan ta’adda kuma jagoran ‘yan fashi da ke kai hare-hare a arewacin Najeriya, musamman jihohin Zamfara, Sokoto da Neja, ya ce gwamnatin Najeriya ba ta da sha’awar kawo karshen ‘yan fashin saboda wasu jami’anta suna amfana da hakan.

Advertisements

Turji wanda ke mayar da martani game da harin bama-bamai da jiragen saman soji suka yi a gidansa na baya-bayan nan ya kuma zargi gwamnati da tunzura su (‘yan ta’adda) don karya yarjejeniyar zaman lafiya da mazauna yankin.
Turji, a farkon wannan shekarar ne ya jagoranci ‘yan kungiyarsa suka yi kisan kiyashi a Zamfara inda aka kashe kusan mutane 200 da suka hada da mata da kananan yara.
A ranar 21 ga watan Agustan bana, mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Sanata Muhammad Hassan Nasiha ya bayyana cewa Turji ya rungumi zaman lafiya. Amma a ranar 18 ga watan Satumba da kyar ya tsallake rijiya da baya a lokacin da sojojin saman Najeriya suka kai harin bam a gidansa da ke kauyen Fakai a karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara lamarin da ya yi sanadin kashe mayakansa da ‘yan uwansa 12.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like