Ya kamata ƴan Nijeriya su hukunta APC ta hanyar hana su ƙuri’a a zaɓen 2023 – Atiku

Advertisements


Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su hukunta jam’iyyar APC,  ta hanyar hana ta kuri’u a zaben 2023 mai zuwa.

Atiku ya yi wannan roko ne a wata wasika ta musamman da ya aikewa magoya bayansa ta email, ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa idan kasa ta kasance mai girma, dole ne ta kasance a hade tare da hadewa. Kuma idan kasa ta kasance mai hadin kai, dole ne ta mallaki shugabancin da ke shirye ya yi aiki bisa manufa.

Dan takarar na PDP ya ce, “Zaben da ke tafe a kasarmu aikin ceto ne domin ceto rayukan al’umma.

“Jam’iyya mai mulki ta APC ta dauke mu kuma mun yi nisa zuwa ga manufar hadin kai da wadata.

Advertisements

Dole ne ceto ran Najeriya ya fara da hana APC kuri’ar ku a 2023. Sun yi mana mummunar illa kuma dole ne a hukunta su kan hakan.

“Amma bai isa a fitar da APC ba. Dole ne mu hada kai cikin PDP – jam’iyya daya tilo da za ta iya ruguza jam’iyya mai mulki.

“Lokacin da kuka zabi PDP, da kun zabi jam’iyyar da ke da tarihin hada kan kasar nan, tare da tabbatar da ci gaban kasa baki daya.

“Don haka, don Allah ku ba ni dama in sake yi muku gargaɗi, da ku ci gaba da tattara ƙarin goyon baya a tsakanin ‘yan uwa, abokai da abokan aikin ku da za su tabbatar da cewa PDP ta yi nasara a zaɓe mai zuwa. Saboda idan PDP tayi nasara duk tamu ce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like