YANZU-YANZU: Rikici ta ɓarke tsakanin Manoma da Makiyaya a jihar Borno

Advertisements

An samu sabani mara dadi tsakanin manoma da makiyaya a jihar Borno, an yi asarar rayuwa sama da 5 a rikicin Hakazalika, an ruwaito yadda aka kone gidaje sama da 40, lamarin da ya jawo shiga tsakani daga hukumomin tsaron jihar An zauna zaman sulhu, hukumomin tsaro da manyan ma’aikatan gwamnati sun zauna don dinke barakar.
 Maiduguri, jihar Borno – Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Abdu Umar ya ce akalla mutane takwas aka kashe tare da kone gidaje 47 a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya saboda shiga gonaki a karamar hukumar Bayo ta jihar. Kwamishinan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar 3 Disamba, 2022 a wani taron da shuganannin kungiyar Miyetti Allah da ta manoma a birnin Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.
Ya bayyana cewa, mutane takwas da aka kashe sun hada da kananan yara uku, inda yace lamarin ba karamin abin damuwa bane ga hukumomin tsaro a jihar. 
Ya kuma shaida cewa, a karshen taron da aka gudanar, za a samar da hanyoyin dike barakar ta hanyar sanya ido kan makiyaya da ke kaura a yankin.
 
Wadanda suka halarci taron An ruwaito cewa, wadanda suka halarci taron sun hada da shugabannin hukumomin tsaro, manyan jami’an gwamnati da shugabannin kungiyoyin biyu da suka samu sabani. Shugaban kungiyar Miyetti Allah MACBAN, Ahmadu Musa-Karube ya ta’allaka faruwar lamarin ga yawaita nome hanyoyoyin shanu a cikin dazuka, Punch ta ruwaito. 
Har ila yau, wakilin manoma, Hassan Musa, shi ma yace tabbas za a daina noma hanyoyin shanu, amma akwai bukatar gwamnatin jihar ta haramta kiwo cikin dare. 
Ana yawan samun sabani tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya, musannan a karshen damina lokutan da ake dauke amfanin gona. Makamancin irin wannan rikicin ya faru a jihar Kano, inda aka samu asara da yawa a wasu kayuka sama da 10 a jihar. 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like