Zaɓen 2023: Yiwa ƴan takara Addu’a baya taɓa ƙimar Malamai – Sheikh Kabir Gombe

Advertisements

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci a Nijeriya Shaikh Muhammad Kabir Gombe ya bayyana cewa yiwa yan takara Addu’a baya taɓa kimar Malamai. Shehin Malamin ya bayyana haka ne a ya yin da Sashen Hausa na DCL Hausa suke zantawa da shi a ranar Litinin.
Malamin yace ba su kadai ne suke yiwa yan takararsu Kamfen ba, har a kan Mambarin Masallacin Juma’a wasu nayi amma ba zaka ji anyi magana a kansu ba; yace abinda yasa shi ne rashin tasirin su a cikin ƙasar.
“Ba malamai kaɗai suke buƙatar kima a Nijeriya ba, yan kasuwa da ma’aikata ma suna buƙatar kima, hakan baya taɓa kimar Malamai” Cewar Sheikh Kabir Haruna Gombe.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like