Babu makawa sai na sayar da matatun Man Fetur idan na zama Shugaban Kasa – Atiku

Advertisements

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen Najeriya na 2023, Atiku Abubakar ya ce zai sayar da matatun man fetur domin samar da kuɗin tallafa wa ƙananan sana’o’i.
A lokacin yaƙin neman zaɓe a Lagos, Atiku ya ce zai samar da kuɗi dala biliyan goma domin tallafa wa matasa su samu aikin yi.
A cewarsa “idan na sayar da matatar mai ta Fatakwal, da ta Warri da kuma matatar mai ta Kaduna.”
Bugu da ƙari a lokacin yaƙin neman zaɓen nasa, Atiku ya ce gwamnatin tarayya ce ta gina birnin Legas ba gwamnatin jiha ba.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like