Majalisa ta gana da gwamnan CBN biyo bayan taƙaita cire kuɗi a bankuna a Nijeriya

Advertisements

Majalisar wakilan Najeriya ta soki sabon tsarin Babban Bankin Najeriya wato CBN, na taikata kudin da za a iya cirewa a banki a rana.
Bisa wannan dalili, majalisar ta gayyaci gwamnan bankin, Godwin Emefiele, ya zo ya mata karin haske da amsa tambayoyi.
A ranar Alhamis din nan ne ya je gaban majalisar kuma ya shaida cewa wannan tsari ba zai yiwu a janye ba, dole a aiwatar kamar yada aka tsara.
Wanan sabon tsari na CBN dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya musamman tsakanin ‘yan kasuwa da sauran al’umma da ke ganin za a kware su.
Sai dai masana na ganin wannan wani kokari ne na takaita yawan mu’amala da takardun kudi a hannu da jan hankali mutane su rungumi tsari hada-hadar kudade ta intanet.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like