Nayi alƙawarin zan canja tsarin Nijeriya in aka zaɓe ni a 2023 matsalarta gudace – Atiku

Advertisements

Osun – Atiku Abubakar wanda shi ne ‘dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa, yace zai yaki rashin tsaro da sauran matsalolin Najeriya. Premium Times ta rahoto Alhaji Atiku Abubakar yana mai shan alwashin da zarar ya shiga ofis, to zai fara aiwatar da tsare-tsaren canza fasalin ƙasa.
Da yake bayani a wajen kamfe a garin Osogbo a jihar Osun, ‘dan takaran yace idan dai ya ci zaben 2023, aka rantsar da shi, to zai kawo sauye-sauye. 
Burin da ke gabanmu kawai shi ne mu ga karshen matsalolin kasar nan na rashin tsaro, rashin hadin-kai, matsin tattalin arziki, rashin ayyukan yi da makoma ta hanyar yi wa tsarin kasa garambawul. 
Nayi maku alkawarin cewa daga ranar farko da na shiga ofis zan fara aiwatar da su. 
Ina kira gare ku, da ku fito kwanku da kwarkwatarku kamar yadda kuka yi a zaben Gwamna, ku zabi jam’iyyar PDP a babban zabe. Ta haka ne kurum makomarku da ta ‘ya ‘yanku za tayi kyau. Ba za mu ba ba ku kunya ba, mu ba APC ba ne, mun yi an gani a baya. 
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like