Advertisements
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC, tace zata fara yaki da yan kasuwa da masu hada man sauya launin domin kawar da su.
DUBA WANNAN: Jarumi Sadiq Sani Sadiq ya mayar da martani bayan Sheikh Idiris Bauchi ya yiwa yan Film wankin babban bargo
Advertisements
Mukaddashiyar babbar daraktar hukumar, Dr. Monica Eimunjeze, ta bayyana hakan, yayin wani taron karawa juna sani da NAFDAC din ta shirya, da hadin gwiwar yan jaridu a fannin lafiya.
Tace hukumar zata fara amfani da karfin ikonta akan shagunan siyar da kayan kwalliya da masu hada maya-mayan bleaching da basa kan ka’ida.
Dr. Monica ta kara da cewa a yanzu maza sun fi mata amfani da man bleaching, wadanda ba’a amince da su ba.