Advertisements
Rahotannin da ke shigo mana yanzu sun bayyana cewa akwai yiyuwar a dawo da gawar Fir’auna a Nijeriya.
DUBA WANNAN: YANZU-YANZU: Hukumar NSCDC ta ayyana ranar da zata fara ɗiban sabbin ma’aikata na shekarar 2022/2023
“Ya kamata a ɗauko gawar Fir’auna daga ƙasar Masar wato Egypt a dawo da ita Najeriya” Cewar Wani ɗalibi mai suna Ashrab Al-Hazard dake karatu a jami’ar al’azhar ta ƙasar masar.
APA Hausa ta rawaito cewa, Yaron yace yana so a dawo da Gawar Fir’auna Nigeria ne Saboda nan ne tafi dacewa a adana ta domin kuwa kusan dukkan ƴan Najeriya kashi 85 basu da gaskiya da kuma tausayin junansu.
Ɗalibin ya bayyana cewar babu inda ake tafka rashin tausayi kamar ƙasar Najeriya kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Instagram.