Advertisements
Rahotannin da ke shigo mana yanzu sun bayyana yadda wasu matasa da ke jihar Nasarawa suka yiwa Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Adamu Tumbur a wajen taron siyasa. Mai Binciken kwakwaf Mahadi Shehu ne ya bayyana wannan bidiyo a shafinsa na Twitter.
Mahadi yace “Shugaban Jamiyyar APC na kasa Abdullahi Adamu ya ga ta kansa a jiya a garin Lafiya jihar Nasarawa, inda aka yi masa tumbur a wajen wani taron siyasa.
A WANI LABARIN KUMA: Hon. Gudaji Kazaure ya bayyana yadda Gwamnan CBN da wasu suka sace Dala Biliyan 171
“Wannan shi ne hausawa ke ce ma raneku dari na barawo, rana daya ta mai kaya. Damokiradiyya ta kara kankama a Nijeriya, Cewar Mahadi Shehu.