Babu wanda ya isa ya yi mani barazana akan wanda na zaɓa a 2023 – Inji Obasanjo

Advertisements

Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya yi masa barazana akan wanda zai zaba a zaɓen shekarar 2023.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a sakatariyar kungiyar Ohanaeze Ndigbo dake jihar Enugu.
A daidai lokacin da ake hasashen cewa Obasanjo yana goyon bayan Peter Obi, jam’iyyar Labour Party, LP, mai rike da tuta, Obasanjo ya ce babu wanda zai iya yi masa barazana kan zaben da ya yi na takarar shugaban kasa.
Obasanjo ya ziyarci sakatariyar ne tare da shugaban kungiyar Afenifere, Pa Ayo Adebanjo da Obi.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like