Wata Gaskiya ta ƙara fitowa game da Kwamitin su Gudaji Kazaure kan CBN

Advertisements

Biyo bayan bidiyon da Hon. Gudaji Kazaure ya yi a ya yin zantawarsa da yan jarida, wanda hakan ya jawo cece kuce ga yan Nijeriya. Har ma Mai magana da yawon Shugaban Kasar Nijeriya, Malam Garba Shehu ya yi martani, inda yace Kwamitin Gudaji Kazaure haramtacce ne ba Shugaba Buhari ya gina shi ba.
Wannan ya sanya wasu takardu suka bayyana, waɗanda ke nuna Lallai Shugaban Kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya haɗa wannan Kwamiti, kuma akwai Gudaji Kazaure ciki.
Haka ya ƙara sanya wa Malam Garba Shehu ya sake martanin cewa “Sanyi Ne Kawai Yake Damun Gudaji Kazaure, Shi Yasa Yayi Furucin Cewar Suna Binciken CBN Kan Badaƙalar Kuɗi, Cewar Shehu Garba
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like