Za a ci tarar masu zagin kuɗin Nijeriya Naira dubu 50 tare da aika su gidan yari – CBN

Advertisements

CBN ta hannun Babbar Manaja, Sashen Ayyukan Kudi ta Babban Bankin CBN, Ms Ngozi Etim ya yi gargadin yan Nijeriya cewa wadanda ke cin zarafin Naira za su iya tsintar kansu a gidan yari. Ya yi wannan gargadi ne a ranar talata.
Ya kuma yi gargadin cewa dokar da ta haramta yin feshi da yaga takardar Naira, musamman a wuraren tarurrukan jama’a na ci gaba da aiki kuma wadanda suka aikata laifin suna da daurin watanni shida a gidan yari ko kuma biyan tarar Naira 50,000.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa sashe na 21 (3) na dokar CBN ta shekarar 2007 ya tanadi cewa karkatar da kudin Naira laifi ne da za a hukunta shi akai.
Babbar Manaja, Sashen Ayyukan Kudi ta Babban Bankin CBN, Ms Ngozi Etim, ta yi wannan gargadin a lokacin da ta zanta da NAN.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like