BINCIKE: Shin ko kunsan amfanin Albasa ga lafiyar jikin ɗan Adam musamman a irin wannan lokacin

Advertisements

Albasa nau’ice ta kayan lambu wadda take dauke da Sinadaran Vitamins da kuma Minerals masu Matukar Muhimmaci da sukeda Matukar bada gudumuwa wajan kara lafiyar jiki dan Adam.
Ga kadan daga cikin Amfanin Albasa ga lafiyar jikin dan Adam:
1. Tana dauke da muhimman sinadarai da suka hada da vitamin C, Folate, potassium, Fiber Wa yanda sukan Taimaka wajan yaki daga bakin kwayoyin cuttuka da kuma daidaita Ruwan jiki.
2. Tana dauke da Antioxidants dasuke taimakawa wajan kara lafiyar zuciya da kuma rage yawan sinadarin Triglyceride da kuma Cholesterol a jiki.
3. Sannan kuma tana rage yawan Hauhawan jini ( high blood pressure ), Saboda Sinadarin Quercetin wanda Flavonoid Antioxidant ne.
4. Albasa tana taimakawa wajan rage hadarin kamuwa ta wasu nau’in cutar Cancer kamar kansar ciki, da kuma ta mahaifa, da kuma hana Kumburi kowane kala ne Sanadiyar sinadaran Cancer fighting properties kamar fisetin da kuma quercetin din da take dauke dasu.
5. Bincike ya nuna cewa Mai ciwon sikari ( Diabetes ) din daya ci Albasa mai nauyi gram 100 na jar Albasa to zai rage mai fasting blood sugar a kalla zuwa 40mg/dl bayan Yan Awanni.
6. Albasa tana kara kwarin kashi da kuma lafiyarsa saboda sinadaran Minerals din da take dauke dasu.
7. Tana taimakawa wajan hana kwayar cutar bacteria girma da suka hada da Escherichia coli (E. coli ), Pseudomonas aeruginosa, Staphylococcus aureus ( S. aureus) and Bacillus cereus da kuma H. Pylori da take haddasa cutar Ulcer. 
8. Albasa tana taimakawa wajan habbaka lafiyar Yan ciki saboda Sinadaran Fiber da kuma Prebiotics.
WRITTEN BY
Abdullahi Ado Popularly Known as Kofa
CEO OF KOFA NUTRI-CONSULT
Nutritionist/Dietitian by Profession
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like