WATA SABUWA: Kimanin Naira Biliyan 30 muka kama a kanta janar Ahmed Idris – EFCC

Advertisements

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati EFCC) ta ce ta kwato naira biliyan 30 daga wurin dakataccen Akanta-Janar na kasar, Ahmed Idris.
Shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka ga manema labarai a fadar shugaban kasar da ke Abuja.
EFCC tana tuhumar Idris da wasu mutane bisa zargin sace N109.
Hukumar na zargin Ahmed da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi.
EFCC ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja.
An kama Idris bayan ya ƙi karɓar gayyatar da EFCC ta rinƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa.
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like